An nada Garkuwa Ibrahim Babuga a matsayin Danmalikin samarin Najeriya

 





Sarkin Samarin Najeriya, Alhaji Sani Uba Daura ne ya amince da nadin bisa sahalewar Mai martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman Adamu, nadin ya guda ne a fadar masarautar Bauchi.

     An baiwa Garkuwa Ibrahim Babuga sarautar Danmalikin samarin Najeriya ne bisa la'akari da jajircewarsa wajen kare martabar matasa tare da aza su a kan turba ta gari ta yadda za su kasance abin alfahari a kasa wajen bayar da gudunmuwarsu ga cigaban taltalin arziki, siyasa da zamantakewa.

     Kazalika, Garkuwa Babuga ya chanchanci wannan sarauta ne saboda kokarin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya da fuskantar juna ba tare da la'akari da banbancin addini, kabila, bangaranci ko banbancin siyasa ba.

     A lokacin da ake nada masa rawani, an bukaci Garkuwa Ibrahim Babuga da ya yi amfani da mukaminsa na Danmalikin samarin Najeriya wajen tabbatar da hadin Kai a tsakanin matasa Kasarnan da Kuma ba su shawarwarin da zasu taimaki rayuwarsu.

       Jim kadan da kammala nadin, Garkuwa Ibrahim Babuga ya bayyana Jin dadinsa bisa wannan sarauta da aka nada shi, ya ce a matsayinsa na Danmalikin samarin Najeriya zai ribanya kokarinsa wajen hada Kai da gwamnati da masarautu domin ganin ana sa matasa a cikin tsare-tsaren cigaba.

     Ya kuma yi kira ga gwamnatin da masautu da shugabannin addini da su kansu matasan da a bashi dukkanin goyon bayan daya dace domin cimma burinsa na ganin matasan Najeriya sun tsere ma tsara a tsakanin takwsrorinsu na kasashen duniya.



Post a Comment

0 Comments